Majalisar Koli ta Musulunci ta nemi a hukunta masu hannu a kashe-kashen Filato

0

Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci a Najeriya, ta yi tir da kashe-kashen da ya sake kunno kai a jihar Filato kwanan nan.

Cikin wata takardar manema labarai da Majalisar ta aiko wa PREMIUM TIMES, kuma Mataimakin Babban Sakatare na Majalisar, Salisu Shehu ya saw a hannu, majalisar ta yi kira da a gaggauta kamo masu hannu wajen kisan a hukunta su.

Majalisar ta nuna takaicin yadda jihar Filato a baya ta ke a matsayin cibiyar zangon zaman lafiya, amma yanzu jihar ta munana da kakshe-kashen kabilanci da addinanci, musammman a kananan hukumomi uku, da suka hada da Barkin Ladi, Riyom da kuma Jos ta Kudu.

Ta bayyana kabilar Kiristocin Birom da cewa su ne manyan ‘yan ta’addan da ke yi wa jama’a kisan kiyashi ta hanyar danne sauran kabilu, musamman Musulmai, yadda abin ya kai har su ka tare musulmai su ka kone su, su na cin naman jikin su a lokutan shagulgulan musulmai.

“Wadannan Kiristocin Kabilar Birom din dai ne masu tare mutane su na kashewa aka gano motar Janar Idris Alkali da wasu motoci a cikin wani babban kandamin da ke yankin su, a Lafendeg Du.

“Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta yi tir da mummunan kisan da aka yi wa Janar Idris Alkali, Zayyanu Shallah, Jubril Mailafia da sauran musulmai a wannan yanki na Lafendeg Du.

“Ganin yadda ya zuwa yanzu aka tsamo motocin matafiya birjik, ciki har da wata mota mai daukar fasinjoji 18, ta Jihar Gombe, Babura 6 da gwarwakin mutane da dama, to mun gano cewa akwai tafkuna akalla kusan 80 a wannan yanki. Wannan ya nuna kenan za a dauki tsawon lokaci kafin a iya gano irin kisan ta’addancin da aka rika yi wa musulmai a wannan yanki a cikin shekaru goma da suka gabata.

“Wannan kisan-kiyashin da ake yi ne ya sa matafiya zuwa Abuja daga Bauchi, Gombe, Yobe, Barno da Adamawa suka gwammace su rika bi ta Kano, su kewaya Kaduna su bulle Abuja. Wannan doguwar tafiyar na daukar su yini daya cur – tafiyar da ba ta wuce awa biyar zuwa shida ba.”

A karshe Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dora laifin kisan Janar Alkali da sauran musulmai da aka kashe a kan kabilar Birom da ke yankin.

Majalisar ta yaba da kokarin da Gwamna Simon Lalong ke yi na tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ta kuma soki wasu kafafen yada labarai da kira na kudancin kasar nan wadanda suke rufe ido, su ke jin kunyar buga mummunar barnar da ake yi wa Musulmai a Filato, musamman rashin bada fifiko wajen batun kisan Janar Idris Alkali.

Share.

game da Author