Mahara sun sace Farfesan Jami’ar Yola

0

Wasu mahara sun sace malamin jami’a a Jami’ar Fasaha ta Modibbo Adama, Yola, mai suna Farfesa Allan Kadams.

An sace Allan makonni kadan bayan sako wani abokin aikin sa da masu garkuwa da mutanen suka yi, bayan sun sace shi.

Rajisata ta jami’ar, mai suna Halima Muhammed, ta shaida wa manema labarai a Yola cewa maharan sun kai farmaki ne a rukunin gidaje na Bajabure da misalin karfe 2 na dare a ranar Litinin, inda suka samu farfesan a gidan sa ya barci. Daga nan suka yi awon-gaba da shi.

Halima ta kara da cewa shugaban jami’an tsaron jami’ar na tattaunawa da iyalan farfesan domin sanin ko wadanda suka yi garkuwa da shi din sun nemi a biya wata diyya kafin su sake shi.

Dama kuma makonni biyu da suka gabata, an yi garkuwa da wani farfesa mai suna Ibrahim Zata, wanda aka gudu da shi daga gidan sa da ke Girei.
An saki Zata bayan an biya diyyar kudade.

Kakakin ‘Yan sandan jihar Adamawa, Othman Abubakar ya tabbatar da samun wannan rahoto kuma ya ce an baza ‘yan sanda domin gano malamin.

Share.

game da Author