Mahara 100 sun far wa kauye Zamfara, sun kashe dan sanda daya da wasu mutane 6

0

A daren Juma’a ne wasu mahara har su 100 suka far wa kauyen Gurbin Bore, dake karamar hukumar Zurmi, Jihar Zamfara inda suka kashe dan sanda daya da wasu su shida.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Muhammed Shehu ya bayyana cewa bayan wadanda maharan suka kashe, sun kona shaguna da wasu motoci.

Muhammed ya kara da cewa tuni har jami’an tsaro da ke aiki a yankin sun fantsama don bin sahun wadannan ‘yan ta’addan ya na mai cewa nan ba da dadewa ba za ya kamo su.

Mataimakin shugaban karamar Hukumar zurmi ya ce shaguna 13 ne maharan suka kona da motoci 15.

Share.

game da Author