Magoya bayan PDP sun yi zanga-zangar haushin zaben fidda gwani a Kaduna

0

Magoya bayan dan takarar gwamna, Idris Mikati na jam’iyyar PDP sun yi zanga-zangar nuna rashin jin dadin yadda aka yi zaben fidda gwanin a jihar Kaduna.

Masu zanga-zangar sun ce ba a yi adalci ba a zaben fidda gwani a Jihar Kaduna.

Sun yi dandazo a sakateriyar PDP ta jihar Kaduna, su na dauke da kwalaye da misalign karfe 11 na safe. Daga nan sai suka mika takardar korafin su ga sakataren jam’iyya na jiha.

Sun dauki kimanin awa uku su na zanga-zangar nuna goyon Mikati.

Sun yi zargin cewa an muzguna wa masu wakilan zabe kuma an yi amfani da kudi.

Shugaban kungiyar masu goyon Mikati, Albab Abdullahi, ya ce wanda suke goyon baya bai taba ficewa daga PDP ba.

Sakataren jam’iyyar PDP Wosono ne ya karbe su kuma ya ce za a duba.

Share.

game da Author