Maganin karfafa garkuwan jiki na dakile yaduwar cutar dajin dake kama nono – Bincike

0

Wasu likitoci daga Jami’ar Salford dake kasar Amurka sun bayyana cewa maganin kara karfin garkuwa a jiki ‘Antibiotics’ mai suna doxycycline na taimaka wa wajen dakile yaduwar cutar dajin dake kama nonon mata.

Likitocin sun bayyana cewa bincike ya nuna cewa maganin na kash kwayoyin cutar dajin da basa jin maganin wanda hakan ke hana cutar sake bullowa a jikin mutum.

” Wannan binciken ya samar wa mata hanyar kubuta kwata-kwata daga wannan cuta.”

A kwanankin baya ne wasu likitocin da suka kware kan cutar daji da lafiyar yara a kasar nan suka bayyana cewa shayarwa da mulmula nono baya hana kamuwa da cutar dajin dake kama maman uwa.

Bamidele Iwalokun shugaban likitocin ya bayyana cewa sun gano haka ne a bincike da suka gudanar don gano haka.

Iwalokun yace sakamakon binciken ya nuna cewa mulmula nono na sa kwayoyin cutar a nono kara girma yadda ya kamata sai dai kuma hakan na taimaka wa wajen gano cutar da wuri.

” Mutane sun dauka cewa shayarwa ko mulmula nono na kare mace daga kamuwa da wannan cutar amma bisa ga wannan bincike mun sami tabbacin cewa lallai ba haka bane.

” Mata da suka kamu da wannan cutar mazajen su ne ke fara ganowa kafin mu likitoci mu sani.”

Iwalokun ya yi kira ga mata da su dage wajen shayar da ‘ya’yan su, mulmula shi akai akai, cewa hakan na taimakawa wajen bada tazarar iyali, rage kiba, kare mace da kamuwa da hawan jini, kara dankon zumunci tsakanin uwa da ‘da.

Share.

game da Author