Wasu likitoci a kasar Amurka sun gano cewa maganin ‘Metformin’ na warkar da cututtukan da akan kamu da su a dalilin shakar gurbataciyyar iska da kuma hana yawan zuban jini idan an sami rauni.
Wadannan ciwo sun hada da cututtukan dake kama zuciya,huhu,shanyewar sashen jiki.
Likitocin sun bayyana cewa sun gano haka ne bayan gwada maganin da suka yi a a jikin wasu beraye.
” Sanin kowa ne cewa maganin Metformin magani ne da masu fama da cutar siga ke amfani da shi amma sakamakon da muka samu a wannan bincike ya nuna cewa maganin na da ingancin kare mutuum daga kamuwa da cututtukan da ake kamuwa da su a dalilin shakar gurbataciyyar iska.
Bayan haka wani likita daga jami’ar Northwestern a kasar Amurka mai suna Chandel ya gano cewa wannan maganin ‘Metformin’ na da ingancin hana yaduwar cutar daji.
Chandel ya gano haka ne shekaru uku da suka gabata.
” A yanzu dai mun san cewa maganin ‘Metformin’ na hana yaduwar cutar daji da samar da kariya daga cututtukan da ake kamuwa da su a dalilin shakar gurbatacciyyar iska sai dai ba muda tabbacin ko wannan magani.
Bincike ya nuna cewa mutane sama da miliyan 100 na amfani da wannan magani a duniya.