Laifuka 9 da Yusuf ya aikata a hukumar NHIS da ya yi sanadiyyar dakatar da shi

0

Shugaban hukumar gudanarwa na hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa Ifenne Enyanatu, ta bayyana cewa kwamitin gudarwa na hukumar ta dakatar da shugaban hukumar Yusuf Usman sai Illa-masha’Allahu.

Enyanatu ta bayyana haka ne cewa kwamitin ta dauki wannan matsaya ne bayan kamashi da laifuka har tara.

1. Kin yin aiki a kasafin kudin hukumar na shekarar 2018

2. Aringizon farashin kudaden na’urori da hukumar za ta siya dake a cikin kasafin kudin.

3. Saka Naira biliyan 30 a hannun jari daga cikin kudaden hukumar ba tare da ya bi doka ba.

4. Hana ma’aikatan hukumar kafa kungiyoyin kare musu hakki.

5. Yin amfani da kudaden hukumar wajen yin balaguron sa a lokacin da aka dakatar da shi a karon farko.

6. Amfani da kudaden hukumar domin siya wa kan sa motocin takama.

7. Babu wanda ya isa ya ce masa tak a hukumar.

8. Rashin tsara hanyoyin samun ci gaba a hukumar duk da cewa kwamitin gudanarwa ta amince masa da yayi haka.

9. Rashin yin amfani da ma’aikatan da ya kamata, Yadda ya ga dama kawai yake yi. Ya tura wancan can ya kawo wannan nan.

Share.

game da Author