Kwararan dalilai 10 da suka wajaba APC ta kori Gwamna Yari daga APC

0

Sanata Kabiru Marafa, dan APC daga jihar Zamfara, ya lissafo wasu kwararan dalilan da ya ce suka wajaba jam’iyyar APC ta kori Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari.

Marafa wanda shi ma ya fito takarar zaben fidda gwanin jam’iyyar APC na gwamnan Zamfara, ya furta wani furuci na baya-bayan nan, inda ya ce Yari ya dauki nauyin wasu masu zanga-zangar neman a cike shugaban APC na kasa, Adams Oshimhole.

DALILAI 10 NA CANCANTAR KORAR GWAMNA YARI DAGA APC

Saboda ya shirya tuggu da husumar da ta haifar wa Kwamitin Gudanarwar APC na Kasa kasa gudanar za zaben fidda gwani a Jihar Zamfara.

2) Saboda ya bada umarni ga jam’iyyar APC ta jiha ta kammala gudanar da zaben fidda gwanin da uwar jam’iyya ta soke, wadda dama ita ce ke da ikon tabbatar da hakan.

3) Saboda ya taimaka kuma ya bude kofa rikici ya barke, wanda ya haifar da rasa rayukan mutane shida, wasu da dama suka samu raunuka, ciki har da mata da kananan yara, a cikin watan Oktoba.

4) Saboda Yari ya muzanta, kuma ya ci mutuncin Adams Oshimhole a fili, tare da yin barazanar tayar da rikici idan wakilan gudanar da zaben fidda gwani daga Abuja ba su yi abin da ya ke so a yi a Zamfara ba.

5) Saboda ya bayyana sakamakon haramtaccen zaben da ya gudanar, bayan da kotu ta bayar da umarnin kada a gudanar da zaben na fidda gwani a jihar Zamfara.

6) Saboda ya toshe wa APC damar fitar da ‘yan takara a zaben 2019 a jihar Zamfara.

7) Saboda ya haifar da gaba da rashin hadin kai a tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC a jihar Zamfara, ta hanyar gudanar da haramtaccen zaben fidda gwani.

8) Saboda ya dauko hayar wasu kungiyoyin bin kadin siyasa har suka fitar da bayanai a kan batun da ke a gaban kotu, wanda ba a kai ga yanke hukunci a kan sa ba.

9) Saboda ya yi watsi da nauyin da ke kan sa na tsayawa ya gudanar da kyakkyawan shugabanci a daidai lokacin da jihar Zamfara ke fama da kashe-kashe, yi wa mata fyade, garkuwa da jama’a, wanda hakan ya ci mutuncin jam’iyyar har ana yi mata wata mummunar fahimta a ciki da wajen Najeriya.

10) Saboda ya kwashi kudin jihar Zamfara ya dauki nauyin gudanar da zanga-zangar neman a cire shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshimhole.

Share.

game da Author