Kotunan Abuja sun saurari kararraki 25,488 a shekara daya –Babban Mai Shari’a

0

Babban Mai Shari’a a Kotunan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Ishaq Bello, ya bayyana cewa kotunan Abuja sun yanke hukunci na shari’u 11,302 daga cikin kararraki 25,488 da suka saurara a cikin wannan shekarar da ta gabata.

Bello ya furta haka ne a lokacin da ya ke jawabi a taron bude sabuwar kakar sauraren kararraki ta 2018/2019, jiya Litinin a Abuja.

Ya ce daga cikin adadin kararrakin da aka saurara a cikin kakar shekarar 2017/2018, guda 12,795 duk kararraki ne da suka yi kwantai tun a waccan shekarar da ta gabata. Kenan ya ce an samu karin kararraki har 12, 693 a shekarar da ta wuce.

Ya zuwa yanzu kuma, Bello ya ce akwai shari’u har 14,186 da ake kan ci gaba da saurare, ba a kai ga yanke musu hukunci ba tukunna.

Ya ci gaba da cewa akwai kararraki 300 da aka cimma daidaiton sasantawa a wajen kotu, ba tare da an kai ga yanke hukunci ba.

Kotunan da wadannan dimbin shari’u ke jibge a hannun su, sun hada kotunan majistare, na ‘Area Courts’ da kuma ‘Customary Courts.’

Share.

game da Author