Kotu ta daure dan acaban dake lalata da yara maza ta baya

0

Kotu a garin Minna jihar Neja ta daure wani dan acaba mai suna Adamu Mohammed a kurkuku bisa zargin kwana da yara maza ta duburan su.

Lauyan da ya shigar da karar Daniel Ikwoche ya bayana cewa Mohammed mai shekaru 23 ya aikata wannan lalata ne a ranar 6 ga watan Oktoba a kauyen Korokpa.

Ikwoche ya ce wani mahaifin yaron da Mohammed ya kwana da shi ta baya ne ya shigar da kara a ofishin ‘yan sanda dake Chanchaga.

” Wani magidanci mai suna Yusuf Buhari ya kawo kara a ofishin ‘yan sanda dake Chanchaga inda ya bayyana cewa Mohammed ya yi lalata da dan sa mai shekaru 10 a dakin sa ta dubura. Bayan mun gudanar da bincike a kai sai muka gano cewa tabbas ya aikata haka.

” Sannan ma, ba wannan yaro shi kadai ya danne ba har da wasu yan yara biyar da ya aikata hakan a kan su.

Ikwoche ya roki kotu da ta yi wa Mohammed sassauci ganin cewa ya amsa laifin sa ba tare da garda ma ba.

Alkalin kotun Nasiru Mu’azu ya yanke hukuncin daure Mohammed a kurkuku na tsawon shekaru hudu.

Share.

game da Author