Mutane hudu daga cikin takwas din da ake nema ruwa a jallo dangane da zargin kisa da bacewar Janar Alkali sun mika kan su ga rundunar ‘yan sandan jihar Filato.
Wadanda suka yi saranda din kuwa sun hada da Basaraken Dura Du,Yakubu Rapp, Timothy Chuwang, Mathew Chuwang da kuma Stephen Chuwang.
Kakakin ‘yan sandan jihar Filato, Terna Tyopev ne ya bayyana cewa sun mika kan su jiya juma’a a hedikwatar ‘yan sandan da ke Jos.
Ya kara da cewa tuni ana ci gaba da yi musu tambayoyi. Kuma ya kara da cewa buga neman su da aka yi ruwa a jallo ya yi tasiri, domin ga shi har hudu daga cikin wadanda ake neman sun yi saranda don kan su.
Kakakin ya ce basarake Rapp ya mika kan sa ranar Juma’a da safe, kuma shi ma ana ci gaba da yi masa tambayoyi.
Discussion about this post