Kira da a karfafa tsaro don kare rayukan ma’aikatan jinkai – Kungiyar Likitoci

0

Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kara maida hankali wajen samar da tsaro yadda y kamata domin kare rayukan ma’aikatan jinkai a kasar nan.

Jami’in yada labarai na kungiyar Obitade Obimakinde ya sanar da haka ranar Laraba a Abuja bayan kisan ma’aikatan kungiyar Red Cross da Boko Haram suka yi.

Idan ba a manta ba a ranar Litini ne Boko Haram suka kashe wata ma’aikaciyar Red Cross mai suna Hauwa Liman.

Boko Haram sun kama ma’aikatan Red Cross, Hauwa Liman, Saifura Khorsa da Alice Loksha a sansanin ‘yan gudun Hijra dake Rann a watan Mayu inda bayan watanni shida suka harbe daya daga cikin ma’aikatan ICRC mai suna Saifura Khorsa.

Daga nan sai Boko Haram kuma suka sake fitar da sanarwar cewa cikin awa 24 za su kashe ma’aikaciyar Red Cross daga cikin wadanda suka kama.

” Muna sane da kokarin da gwamnati ta ke yi game da ceto Hauwa amma dole gwamnati ta gane cewa ingata fannin tsaron ta zai taimaka wajen kawar da duk wannan matsaloli na rashin tsaron da ake fama da shi a kasar nan.

Share.

game da Author