Kawunan Sanatoci ya rabu saboda bangaranci a nada manyan jami’an tsaron gwamnatin Buhari

0

A yau Talata ne wasu sanatoci a Majalisar Dattawa suka rika tayar da jijiyar wuya dangane da bangaranci a nadin shugabannin tsaro na Majalisar Tsaro ta Kasa.

Yayin da wasu ke cewa kiri-kiri da gangan Shugaba Muhammadu Buhari ya maida yankin Kudu Maso Gabas saniyar-ware, ya ki daukar shugabannin tsaro daga yankin, wasu kuma na cewa Buhari ya yi daidai domin ya yi amfani da tsarin raba daidai da gwamnatin tarayya ke la’akari da shi.

An fara wannan zazzafar tankiya a lokacin Sanata Victor Umeh, dan jam’iyyar APGA daga jihar Anambra ya gabatar da kudirin cewa akwai bukatar a nada dan yankin Kudu masu Gabas a cikin Majalisar Tsaro ta Kasa.

Umeh ya nuna damuwar sa ganin babu dan shiyyar su ko daya a Majalisar Tsaro ta Kasa da kuma Majalisar Hafsoshin Tsaro ta Kasa.

Sanata Enyinnaya Abaribe dan PDP gada jihar Abia, ya zargi Buhari da maida shiyyar su saniyar-ware.

Har ya jawo wata aya ta 5 (1) A da B a cikin kundin tsarin mulkin kasa, ya yi wa Buhari wa’azi da jan hankali daga abin da ayar ta kunsa.

Sai dai kuma Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye, Bala Ibn Na-Allah, ya fatattaki wanda ya kawo kudirin, ya ce ya yi wa kundin tsarin mulki mummunar fassara.

“Dokar kasa ta 219 ta ce kafin shugaban kasa ya ba su umarnin kama aiki, duk shugabannin hukumomin da zai nada sai ya kawo sunayen su gaban Majalisar Dattawa an amince da su, kuma Buhari duk ya yi haka.’’

Na-Allah ya ce majalisa ta amince da su, don me ne kuma yanzu Sanata Umeh zai fara wani kartar kasa ya na tayar da jijiyoyin wuya bayan sama da shekara uku?

Ya ce kuma Buhari bai maida kowane yanki saniyar-ware ba.

Shi ma Sanata Barau Jibrin ya yi wa Umeh hayagagar cewa abin da ya fada ba gaskiya ba ne, domin Ministan Harkokin Waje dan yankin su ne.

Saboda an kasa cimma matsaya guda kai ya fara hayaki, sai Shagaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya jingine batun zuwa wata rana ko lokaci.

Share.

game da Author