Kashi 69 na yara a Najeriya ba samu damar yin ilimin Boko ba – UNICEF

0

Jami’ar asusun tallafa wa yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) Pernille Ironside ta bayyana cewa kashi 69 bisa 100 na yaran Najeriya basu da ilimin boko.

Jihar Bauchi ce ke da yawan yara har miliyan 1.1 da ba su makaranta boko sannan jihar Katsina da ke bi mata da yara 781,500.

Ironside ta fadi haka ne a taron da UNICEF ta shirya domin hada hannu da sarakunan gargajiyya don kawar da wannan matsalar.

An gudanr da wannan taro ne a jihar a Kaduna.

Ta ce bincike ya nuna cewa adadin yawan yaran da basu da ilimin boko a Najeriya gaba daya ya kai miliyan 10.5 wasu binciken kuwa sun nuna cewa yawan ya kai miliyan 13.5. Sannan ta kara da cewa za su ci gaba da taimakawa wajen ganin ana wayar wa iyaye kai musamman a karkara domin su saka ‘ya’yan su a makarantun gwamnati.

A karshe Ironside ta jinjina goyan bayan fanin ilimi da wasu sarakunan gargajiya ke yi kamar su sultan din Sokoto da sarkin Kano sannan da yi kira ga sauran sarakunan da su hada hannu da su don ganin sun cin ma burin su.

Share.

game da Author