Hukumar USAID ta bayyana cewa jihar Kogi na daga cikin jihohin Najeriya da mata ke gudun yin amfani da dabarun bada tazarar iyali.
Jami’in hukumar Gabriel Alobo ya sanar da haka a taron samun madafa da aka yi a Lokoja. sannan ya kara da cewa kashi 11 bisa 100 na dabarun bada tazarar iyali ne ake amfani da su a jihar.
Ya ce taron ta tattauna wasu matsalolin da ke hana mata yin amfani da dabarun bada tazarar iyali da suka hada da rashin wayar da kan mutane, rashin isassun dabarun bada tazarar iyali, rashin horas da ma’aikata da dai sauran su.
” A lissafe kudaden da za mu yi amfani da su domin wayar wa mata a jihar kai game da amfanin dabarun bada tazarar iyali a jihar zai kai Naira miliyan 500.
A karshe kwamishinan kiwon lafiya na jihar Saka Audu ya bayyana cewa jihar na da asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 247 dake bada dabarun tazarar iyali a jihar.
” Duk da haka gwamnati za ta kara gina asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya domin tabbatar cewa dabarun bada tazaran iyalin da ake amfani da su a jihar ya karu daga kashi 11 zuwa 20 bisa 100’’.
Discussion about this post