KANKANTAR ALBASHI: Gwamnoni sun amince da naira 22,500, Kungiyar Kwadago ta ce bata yarda ba

0

Gwamnonin Jihohi 36 sun amince da naira 22,500 a matsayin mafi kankantar albashi.

Gwamnonin sun amince da wannan tayin ne a jiya Talata, bayan kammala wani taron gaggawa da suka yi a Abuja.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Abdul’aziz Yari na jihar Zamfara ne ya bayyana haka bayan tashi daga taron.

An tunanin cewa Kungiyar Kwadago ta Kasa ba za ta amince da wannan matsaya ta gwamnonin ba, domin su sun jajirce ne sai dai a biya naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi.

Sun kuma yi alwashin fara yajin aiki tun daga ranar 6 Ga Nuwamba, wanda rahotanni a jiya Talata sun tabbatar da cewa sun fara shirye-shiryen tuntubar rassan kungiyar na jihohin kasar nan domin fara shirin yajin aikin.

Sai dai kuma abin da kamar wuya domin kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta ki amincewa da Naira 22,500 din da kungiyar gwamnonin suka amince da shi.

Kungiyar gwamnonin sun ja labule ne ranar Talata domin samar da matsaya daya game da albashin da za su iya biyan ma’aikata.

Sai dai matsayar da kungiyar gwamnonin ta sanar bai yi wa kungiyar NLC dadi ba domin yanzu kuwa kungiyar ta canja shawara ma daga Naira 30000 din da suka ce gwamnati ta amince kuma suke bukata zuwa Naira 66,500.

” Yanzu Karin da muke bukata daga wajen gwamnati ya karu daga Naira 30,000 zuwa Naira 66,500.

Share.

game da Author