Jirgin sama ya kama wata a filin jiragen Lagos

0

Wani jirgin sama mallakar kamfanin Overland Airways ya kama da wuta yau Juma’a a filin saukar jirage na Murtala Mohammed Airport, Lagos.

Jirgin ya kama da wuta ne a inda ya ke ajiye a kebantaccen filin ajiye jirage.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, Ya ruwaito cewa jirgin mai lamba 5N-BPE, ya kama da wuta ne a lokacin da ake zuba masa mai.

An ce jirgin ya fara cin wuta kenan sai jami’an kashe gobara da ke jiran tsammani a filin jirgin suka gaggauta kashe wutar.

Hukumomin filin jirgin da jami’in kamfanin sun tabbatar da cewa barnar da wutar ta yi ba ta yi muni sosai ba.

sama ya kama wata a filin jiragen Lagos

Share.

game da Author