Bayanan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta fitar kan wasu ‘yan takarar shugabancin kasar nan, ya nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kasa gabatar wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, takardar sa ta jarabawar kammala sakandare, wato WAEC.
Buhari wanda ke neman sake nasara a zaben 2019, ya shaida wa INEC a rubuce cewa takardar sakamakon kammala sakandare din sa ta na hannun hukumar tsaro ta sojoji.
Jiya Alhamis ne INEC ta lika sunayen ’yan ntakarar mukamai daban-daban daga jam’iyyu 70 daga cikin 91 da suka yi rajista, ciki kuwa har da sunan Muhammadu Buhari dan takarar shugaban kasa a karo na a karkashin jam’iyyar APC.
Jerin sunayen da INEC ta gabatar wa manema labarai ya tabbatar da cewa Buhari ya kasa gabatar da takardun sa na tabbatar da ya rubuta jarabawar WAEC ko bai rubuta ba, ya ci ko bai ci ba.
Sai dai kuma ya hada da rantsuwa a kotu, inda ya bayyana cewa:
“ Ni ne mai wannan suna a sama, kuma ni ne na yi wannan rantuwa cewa takardun bayanai nan a kammala sakandare da kuma jarabawar kammala sakandare, wadanda na cika tun a zaben shugaban kasa na 2015, duk su na hannun hukumar tsaro ta sojoji.
Amma kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar da kwafen takardun sa na shaidar kammala difiloma a kan fannin shari’a, da ya kammala cikin 1969.
YADDA AKE SUKA DA CACCAKAR BUHARI
’Yan Najeriya da dama, musamman har da masu adawa, sun maida martani da kuma tofa albarkacin bakin su dangane da yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kasa gabatar wa INEC da takardun kammala sakandare da kuma shaidar ya rubuta jarabawar WAEC.
Dama ko a cikin 2015 kafin zabe, sai da takarar kammala sakandare din Buhari ta janyo masa cece-ku-ce. To a yanzu da zai sake tsayawa takara ma, ya kasa gabatar da takardun ga INEC, sai dai ya aika da rantsuwa daga kotu cewa ya rantse da kwansitushin din Najeriya takardun sakandaren sa su na hannun hukumar tsaro ta sojoji.
’Yan Najeriya da dama sun hau Buhari da sara, yakushi, karta, cizo har da caccaka, amma duk da fatar baki, inda suka rika nuna mamakin a matsayin sa na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya ba zai iya umartar sojoji su ba shi sakamakon takardun sa na sakandare ba, tunda zai yi amfani da su a abu mai muhimmanci, wato zaben shugaban kasa.
BUHARI BA ZA MU YARDA DA ‘NEPA BILL’ BA -Kakakin PDP
“Idan kai mai gaskiya ne, to abin da ya dace ya yi shi ne ka rubuta wa hukumar sojoji wasika, ka ce su ba ka takardun ka na WAEC, ba wai ka yi wa INEC rantsuwa da kwansitushin ba. Domin ai ko magoya bayan ka ba za su amince da takardar biyan kudin NEPA a matsayin satifiket na rubuta jarabawar WAEC ba. Haba Oga, ina satifiket din ka?” Inji Kola Ologbondiyan, a shafin sa na twitter.
DAMA CAN BUHARI BA SHI DA SHAIDAR WAEC -Reno Omokri Tsohon hadimin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, a kan yada labarai, Reno Omokri ya bayyana cewa abin da Buhari ya yi a 2015 da 2019 ya tabbatar da cewa dama can bai mallaki takardun kammala sakandare da na sakamakon rubuta jarabawar WAEC ba.
“A wannan kakar zaben ma Buhari ya ce takardun sa na wurin sojoji? Tabdijan! To sojojin a karkashin wa suke? Mu fa ba za mu karbi wannan uzirin ba
Ina son kowa ya fito domin a tirsasa Buhari sai ya fito da sakamakon jarabawar sa ta kammala sakandare, WAEC.”
WA ZAI DAUKE NI AIKI IDAN BA NI DA SATIFIKET NA KARATU? –Agbang Mercy
Wata mai suna Agban Mercy kuwa ta cika da mamaki, har ta yi tambaya da kuma kalubale da ’yan Najeriya cewa yanzu a fito a fada mata gaskiya idan ba ta da takardun kammala makaranta, wa zai iya daukar ta aiki?
Tun daga kan tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, har zuwa sauran jama’a daidaiku, kowa daga mai tambayar yadda aka yi wannan sakaci, sai mai jefa tababar cewa da wuya idan Buhari ya rubuta jarabawar, sai kuma masu cewa ba za ta sabu ba, wai bindiga a ruwa. Wasu kuma na ta cewa da sakyal, wai an raba nama an ba mai kaza kai.
Da dama a shafin twtter sun ce ba su ga amfanin fallasa wadanda ba su da katin NYSC da ake yi ba, alhari ga shugaban kasa dungurugum ba shi da katin kammala sakandare, wato jarabawar WAEC.