Jam’iyyar APC bata ginshe mu ba, Buhari ya ci gaba kawai – ‘Yan Najeriya

0

Mafi yawa-yawan ‘yan Najeriya da suka amsa tambayar ko jam’iyyar APC ta ginshe ‘yan Najeriya har ana bukatar PDP ta dawo ko a’a sun zabi, a ci gaba a haka.

Kusan kashi 65 bisa 100 na sama da mutane 200 da suka fadi ra’ayin su a shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/premiumtimeshausa/ sun bayyana cewa duk da kuka da ‘yan Najeriya ke yi bisa halin rayuwa, sun gwammace mulkin ta ci gaba a karkashin jam’iyyar APC.

Ko da yake da dama sun bayyana nasu ra’ayin cewa canjin shine mafita ga kasa.

Karanta wasu daga cikin ra’ayoyin masu karatu

Aboubakar Sadikk: wallahi kada Ku yarda da PDP mayaudara ne kawae . muyi hakuri da halin da muke ciki yanxu idan muka bari PDP suka hau mulki to sai mun gwammaci bama Raye wlh…

Balkisu Ibrahim: Ai APC yanzu muka fara yinta.babu gudu bajadabaya.Nigeria sai Baba Buhari 2019 insha Allah.

Hamisu Alhassan: Wlhi ni takaicina shine a rika nuna mun atiku a matsayin Dan tskarar Nigeria. Ai wlhi kisan da su atiku sukayiwa Nigeria irinsu buhari dari masu kishin kasar su basu iya gyara ta. Dawa yau na nasan kafin mulkin PDP a Nigeria akwai kampanoni da kadarorin gwamnati wanda su atiku da Obj suka tarwatsa irinsu Nigeria air way, nitel, ajakuta da daga baya bayan nan harda nepa. Da hankalina sai ka kawo atiku kace na zabeshi.

Adams Babangida: Da ace gwamnatin APC da shugaba #Buhari sun tabuka abin kirki da yanzu a kasar nan babu wanda yake batun PDP, rashin tabuka abin azo a gani shiyasa mutane suka koma neman machechi a PDP.

Khadijah A Abdul Salam: Mufa babu ruwanmu da jam’iyyarka matukar zakayiwa yan kasa aiki.
BUHARI ya Gaza sbd haka zamu sauyashi insha Allahu

Bappa Ahmed Mohammed: Ai inkaga buhari baici zabeba toh saidai inya shanza sunansa yace sunansa ba buhariba amma insha Allahu babu abundazaikadaci dayardar Allah muje zuwa pmb

Nabilat Nabeelat: Ai’idan maganar yaudara akeyi to apc itace tudundawar makaryata da mayaudara kuna maganar pdp shin apc mene ba’a aikataba acikinta ? sabodahaka dukgautan jane

Share.

game da Author