Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta yi gargadi ga dukkan ‘yan takara da daukacin jam’iyyun siyasa cewa lokacin fara kamfen bai yi ba tukunna.
Shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Mahmood Yakubu ne da kan sa ya yi wannan gargadin a cikin wata takarda da ya karanta, yayin da ya ke jawabi a gaban wasu kwararrun masana zabe daga Kasashen Afrika Rainon Ingila.
An shirya wannan taro ne na hadin guiwa, tsakanin Kungiyar Kasashe Rainon Ingila da kuma INEC.
“Bari kuma na tunatar da jam’iyyun siyasa da dukkan ‘yan takarar mukamai daban-daban cewa kammala zabukan fidda-gwani ba wai ya na nufin a tafi a fara kamfen ba ne. Dokar Zabe ta 99(1), ta ce ba za a fara yakin neman zabe ba sai ana saura kwana 90 cur a gudanar da zaben da zai gudana.” Inji shugaban INEC.
Tantebur din ranakun zabe da kuma dokar zabe ta kasa sun nuna kenan sai a ranar 18 Ga Nuwamba, 2018 ne za a fara yakin neman zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya.
Yayin da da sai a ranar 1 Ga Disamba ce za a fara yakin neman zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki na jihohi.
Yakubu ya yi kira da a bi wannan ka’ida sau da kafa, ba tare da wani dan takara ko jam’iyya ta karya wannan doka ba.
Wannan gargadi na shugaban hukumar zabe, ya zo ne kwana daya bayan da aka kammala zaben fidda gwanin ‘yan takarar shugaban kasa da na gwamnoni.
Hukumar zaben ta kuma bayyana ranakun da za ta fara da kuma rufe karbar fam na ‘yan takara da ta ce jam’iyyun siyasa su kai ofishin ta.
Ya ce za a fara karbar fam na ‘yan takarar shugaban kasa da na majalisar tarayya a ranar 10 Ga Oktoba, sannan a rufe karba a ranar 18 Ga Oktoba, 2018.
Yakubu ya kara nanata cewa daga ranar 22 Ga Oktoba za a fara karbar fam na ‘yan takarar gwamnoni, a rufe ranar 2 Ga Nuwamba, 2018.
Hukumar zaben ta ce za ta rika zama a Babban Dakin taro na International Conference Center daga 9 na safe zuwa 4 na yamma a kowace rana, domin zaman karbar fam din.
Farfesan ya ce tuni hukumar zabe ta sanar da dukkan jam’iyyun siyasa cewa ba za ta kara ko da wa’adin yini daya ba, idan har lokacin karbar fam din ya wuce.
Daga nan sai ya kara da cewa duk wani fam da za a kawo, tilas a hado shi da wasika wadda shugaban jam’iyya da sakataren sa suka sa wa hannun tabbatar da amincewar wannan dan takara, kamar yadda ya ke a tsarin doka.