Ina ja maka kunne, kul ka fara, APC marmari daga nesa ne – Shehu Sani ga Ekweremadu

0

Sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya gargadi mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da kada yayi wa kasan sa sakiyar da ba ruwa, ya ce zai fice daga PDP ya koma APC.

Shehu ya tura wa Ekeremadu wannan sako ne ta shafin sa ta tiwita.

Shehu Sani ya ce shine zai ba da labarin abinda ya gani a APC domin shine na karshen tattara kayan sa ya fice daga jam’iyyar.

” Dan-uwa, ka ci gaba da zama a inda kake abinka salin-alun. Ni ma kwanannan na ware. Amma idan kaki ji, jiki magayi.

Koda yake tuni ma shi kan sa mataimakin shugaban majalisar dattawan Ekweremadu ya fadi kuru-kuru cewa bashi da wannan shiri a lissafin sa na siyasa.

Share.

game da Author