Hukumar FCT ta dauki nauyin karatun yarinyar da hatsarin jiragen sama ya ji wa rauni

0

Hukumar Mulkin Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta bada sanarwar daukar nauyin karatun Elizabeth Elijah daga Sakandare har kammala jami’a, sakamakon raunin da ta ji, lokacin da wani burbushin jirgin yakin sojoji ya fado mata a kafa, a lokacin da hatsarin ya auku.

Daraktan Hukumar Kula da Ilmin Bai Daya (UBEC), Adamu Noma ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai wa yarinyar ziyara a Babban Asibitin Maitama, a jiya Laraba, a Abuja.

Ya ce hukumar mulki ta FCT ta yanke shawarar daukar nauyin karatun yarinyar ne daga lokacin da aka sallame ta daga asibiti.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa a lokacin da hatsarin ya afku, Elizabeth ta na gona, a kusa da Mpape, inda wani burbushin jirgin yakin ya fado mata a kafa.

Noma ya ce hukumar FCT ce za ta rika saya mata litattafai, biya mata kudin makaranta, kayan makaranta, takalmi da duk wani abu da makaranta za ta bukata daga gare ta.

Daraktan Hukumar Daukar Nauyin Dalibai na FCT, Ahmad Rani ya tabbatar wa PREMIUM TIMES wannan labari.

An tabbatar da cewa yarinyar ta na samun sauki daga raunin da ta ji da kuma kidimewar da ta yi. Za a sallame ta kwanan nan.

NAN ta samu labarinn cewa yarinyar mai shekaru 15, ta fito ne daga jihar Kaduna, a garin Kachia, amma ta na zaune tare da ‘yan uwan ta a kauyen Chikoko da ke cikin Karamar Hukumar Bwari, Abuja.
Ta kammala firamare, amma rashin wadata ya sa iyayen ta suka kasa daukar karatun ta zuwa sakandare.

Ko a lokacin da hatsarin ya auku, mahaifin ta ba shi da kudin da zai hau mota daga kauyen zuwa cikin garin Abuja domin zuwa asibiti ya duba ta.

Share.

game da Author