HARKALLAR GANDUJE: ’Yan sanda sun hana dalibai yi wa Gwamnan Kano zanga-zanga

0

Hukumar ‘Yan sandan Jihar Kano ta hana Kungiyar Daliban Jami’o’i ta Jihar Kano (NANS) gudanar da zanga-zanga a kan badakalar karbar milyoyin daloli da ake zargin Gwamna Abdullahi Ganduje ya aikata.

An rika nuno Ganduje na karbar kudade a hannun wasu da ake zargin ‘yan kwangila ne.

Yayin da Ganduje ya karyata yace sharri ne, PREMIUM TIMES ta yi amfani da kwararrun ta wajen bin diddigin bidiyon, ta kuma tabbatar da sahihancin sa, kamar yadda Daily Nigerian ita ma ta tabbatar.

Kakakin Yada Labarai na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Magaji Majiya, ya bayyana cewa an ki bai wa daliban iznin gudanar da zanga-zangar ce da suke nemi shiryawa a ranar 29 Ga 0ktoba, daga kan titin Zoo Road zuwa Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Majiya ya ce daliban sun rubuto cewa za su yi zanga-zangar ne domin su nemi Ganduje ya sauka ya bari masu bincike daga waje masu zaman kan su su yi aikin bincike, ba tare da yi musu katsalandan ba.

Majiya ya ja kunnen shugaban daliban, Kwamared Isa Abubakar, da ya ja hankalin sauran mambobin kungiyar kada su kuskura su fito yin zanga-zanga.

Ya shawarci duk mai korafi ya tunkari kwamitin da majalisar dokokin jiha ta kafa domin ya binciki zargin da shawarwarin sa a rubuce.

Share.

game da Author