Kungiyar jin kai ta Amnesty International’, ta yi kira ga hukumomin tsaron kasar nan da su tabbata sun samar wa mawallafin jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar tsaro na musamman.
Jami’in kungiyar Osai Ojigho ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, sannan ya kara da cewa tun da jaridar Daily Nigerian ta saki wani bidiyo dake nuna gwamnan jihar Kano, Ganduje, yana karkacewa ya na loda daloli a aljuhunsa daga hannun wani dan kwangila Ja’afar yaya fara samun sakonni masu yin barazana ga rayuwar sa wanda a dalilin haka ya fara wasan lambo.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne jaridar Daily Nigerian ta saki wani bidiyo dake nuna gwamnan jihar Kano, Ganduje, yana karkacewa ya na loda daloli a aljuhunsa daga hannun wani dan kwangila.
Ja’afar ya bayyana wa kwamitin dake zama a Kano yau, Alhamis cewa ya dade yana bibiyar gwamnan tun bayan da abokin sa da yake dan kwangila ne ya sanar masa da yadda gwamnan ya rika karbar cin hancin kashi 15-25 bisa 100 na duk kwangilan da ya bada a jihar Kano.
” Bayan nan sai na nemi shi dan kwangilan ya saka na’urar daukan hoto a jikin rigar sa. Mun dauke sa sama da bidiyo dabam dabam har kala 10 wanda kusan duka suna nuna fuskarsa da yadda yake ta karkacewa ya zura bandir-bandir din daloli a aljihun sa.
Ja’afar ya mika wa kwamitin wasu bayanai da zai tabbatar da aikin sa.