HARGITSI: ‘Yan sanda sun fesa barkonon tsohuwa a wurin zaben fidda-gwanin sanatocin APC a Jigawa

0

Rincimi ya yamutse a yayin da ake gudanar da zaben fidda-gwanin jam’iyyar APC na sanata a Karamar Hukumar Hadejia ta Jihar Jigawa.

Hargitsin ya nemi yin muni, har sai da ta kai ‘yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa akan masu zabe da shugabannin jam’iyya domin a samu lafawar yamutsin.

Wannan rikici ya faru ne wurinn zaben dan takarar sanata a shiyyar Jigawa ta Arewa, wanda aka gudanar a filin wasan kwallon kafa na garin Hadeja.

Barkewar rikicin ya faru ne bayan da wasu masu zabe suka fara korafin cewa an baddala sunayen wadanda za su jefa kuri’a.

Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Ibrahim Hassan na daga cikin wadanda ke neman takarar sanata. Akwai kuma Ahmed Garba, Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Jigawa da kuma Mohammed Husseini.

Daga Husseini ya bayyana janyewar sa daga takarar a dalilin zargin da ya yi cewa an cusa sunayen masu zabe wadanda ba halastattu ba.

A lokacin da ake rubuta wannan labari, mataimakin gwamna da kuma Garba su na ganawa da jami’an tsaro, wadanda suka kulle filin zaben fidda-gwani, suka hana kowa shiga.

Share.

game da Author