Kakakin Yada Labaran Jam’iyyar APC na Kasa, Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewa masu suka da neman a tsige shugaban jam’iyyar, Adams Oshimhole, musamman wasu gwamnoni da manyan jami’an gwamnati, suna yi ne kawai saboda sun fadi zaben fidda gwani, ko kuma a ce jama’a ba su zabi wadanda su ke so ko suka tsaida don son su ba.
Da ya ke zantawa da manema labarai, Lanre ya yi kakkausar suka a kan wasu gwamnoni, musamman na jihar Ogun, Ibikunle Amosun, wanda ya kira Oshiomhole ‘dan gada-gada.’ Sai kuma ya nuna fushin sa kan Shugaban Gidan Radiyon Muryar Najeriya, wanda ya kira Oshiomhole ‘dan damfara.
JIHAR IMO
Da ya ke magana a kan dan takarar gwamnan APC a jihar Imo, inda ake zargin Gwamna Rochas Okorocha ya yi karfa-karfa da banga-bangar dora sirikin sa, Uche Nwosu, Lanre ya ce har yau APC ba ta kai ga yanke hukuncin wane ne dan takarar gwamna a jihar Imo ba tukunna.
Ya yi nuni da cewa ranar 2 Ga Nuwamba ne wa’adin mika wa INEC sunan dan takarar gwamna a kowace jiha zai cika, ba ranar 18 Ga Oktoba kamar yadda INEC din ta rika jaddadawa ba.
“Kun san cewa rigimar wane ne dan takarar gwamnan APC a jihar Imo ta na kotu. Don haka ba mu da dan takara tukunna. Amma duk irin sakamakon hukuncin da kotu ta zartas, mai dadi ko maras dadi, to za yi amfani da shi, ta hanyar bin umarnin kotu.”
Jam’iyyar APC na fuskantar barazanar yiwuwar kasa tsaida dan takarar kowane zabe a jihohin Zamfara, Rivers da Imo, da kuma wasu ‘yan takara da dama a daidaikun jihohi.
Discussion about this post