Har yanzu ba a janye dokar hana zanga-zanga a Filato ba na nan ba -Gwamnati

0

Gwamnatin Jihar Filato ta kara jaddada cewa har yanzu doka hana gudanar da taruka da ya hada har da zanga-zanga na nan daram ta na aiki a jihar, kuma ta kara gargadin cewa jama’a su ci gaba da kiyaye dokar.

Kwamishinan Yada Labarai Yakubu Dati ne ya bayyana haka, a yau Litinin.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ya ruwaito cewa an ga tashin wata ‘yar zanga-zanga, tun bayan hargitsin da ya tashi sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar 10 Ga Oktoba.

Jim kadan bayan kammala fadin sakamako ne sai hasalallun matasa suka kone ofishin shugabar riko ta karamar hukumar Bassa, Sarah Bali, su na masu zargin cewa an tafka magudi.

A karamar hukumar Mangu ma an yi zanga-zangar nuna fushin zargin baddala sakamakon zabe.

Dati ya ce an hana gudanar da zanga-zanga, kuma an nada kwamitin sauraren korafe-korafen zabe.

Share.

game da Author