Hukumar Kula Da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), ta umarci hukumomin jin dadin mahajjata da ke jihohi 36 da Abuja, cewa su fara yin rajistar maniyyata aikin Hajjin 2019 ta intanet tun daga yanzu.
An dauki wannan mataki ne bayan zaman da aka gudanar tare da jihohi inda aka cimma daukar wasu matakai da dama tsakanin Hukumar ta Kasa da kuma Hukumomin Jin Dadin Alhazai na jihohi.
An gudanar da wannan taro a karshen makon da ya gabata a Abuja.
Wannan umarni na cikin takardar manema labarai da kakakin yada labarai ta NAHCON, Fatima Usara ta fitar.
Ta ce an gano cewa jinkirin da ake samu wajen kasa kammala rajistar maniyyata a kan lokaci ya na daya daga cikin abin da ke kawo cikas wajen samun gagarimar nasarar tafiyar da harkokin mahajjata daga Najeriya.
A wurin taron, an kuma yanke shawarar aza naira miliyan 1.5 a matsayin kudin kujerar tafiyar aikin Hajjin 2019.
Ta kara da cewa idan maniyyaci ya fara biyan kudin da guntu-guntu ta online, to zai kammala biya gaba daya a cikin watan Fabrairu, 2019.
Ta ce za a caji naira 500 kacal ga wanda zai yi rajista da biyan kudin aikin Hajjin 2019 ta online.
Kudin cajin na naira 500 kuma an riga an saka su a cikin jimlar kudin kujerar aikin Hajji din.
Discussion about this post