Hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa ta yi barazanar fara yajin aiki daga ranar 6 ga watan Nuwamba

0

A ranar Lahadi ne kungiyoyin kwadago na kasa (NLC da ULC) suka yi wa gwamnatin tarayya barazanar shiga yajin aiki daga ranar 6 ga watan Nuwamba idan har gwamnati bata biya bukatun su ba.

Shugaban NLC Ayuba Wabba da ULC Joe Ajaero suka sanar da haka wa manema labarai.

Kungiyoyin sun bayyana cewa daukan wannan matsaya ya zama dole musamman yadda gwamnati ke neman bujirewa yarjejeniyar da suka amince a kai na biyan karancin albashi Naira 30,000.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne kungiyar kwadago ta shiga yajin aiki a dalilin rashin ce musu uffan gwamnati ba ta yi ba.

Wabba ya ce a tattaunawar da suka yi da gwamnati wanda gwamnonin jihohin kasar nan shida suka halarta gwamnati ta yarda ta biya Naira 30,000 a matsayin karancin Albashi.

” Gwamnati ta musanta haka inda ta bayyana cewa matsayar da aka yi a wannan zama shine gwamnatin tarayya za ta biya ma’aikatanta Naira 24,000 sannan na jihohi su biya Naira 20,000.

Share.

game da Author