GYARAN FASALIN KASA: Gwamnatin Buhari ta yaudari ’yan Najeriya –Shehu Sani

0

Tsohon Sanatan jam’iyyar APC, wanda ya koma PRP, Shehu Sani, ya bayyana cewa gwamnati Shugaba Buhari ta yaudari ’yan Najeriya game da batun sake fasalin kasar nan.

Ya bayyana a shafin sa na twitter cewa duka dai gwamnatin PDP da ta gabata ta kauda kai daga batun sauya fasalin kasa, ita kuma gwamnatin Buhari yaudarar jama’a ta yi a kan batun.

Wannan bayanin na sa ta taso ne sakamakon cacar-baki da ake kan yi tsakanin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ba kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a kan batun sake fasalin kasa.

Shi ma Atiku ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa, tsakanin 1999 zuwa 2007, a karkashin mulkin Olusegun Obasanjo a jam’iyyar PDP.

Yayin da Atiku ke yin kamfen a kan kudirin gyaran fasalin Najeriya, Osinbajo ya na mai cewa Atiku da wata manufa ya ke yin kamfen din.

Idan za a iya tunawa, daga cikin alkawurran da APC ta yi wa ’yan Najeriya kafin a yi zabe, har da alkawarin sake fasalin kasar nan idan ta ci zabe.

Sai dai kuma tun bayan cin nasarar zaben a 2015, APC ta kauda kai daga batun, ko tayar da maganar ba ta son a na yi.

Share.

game da Author