Gwasale Akpabio: Yadda sanatoci suka rika murza gashin baki a Majalisar Dattawa

0

An yamutsa gashin baki yau Laraba a Majalisar Dattawa, yayin da Shugaban Majalisar, Bukola Saraki ya gwasale tsohon Shugaban Marasa Rinjaye, Godswill Akpabio.

Hakan ta faru ne a lokacin da Saraki ya hana Akpabio damar yin jawabi daga inda ya ke zaune, a bisa hujjar cewa ba wurin zaman sa ba ne, ba zai yiwu ya yi magana daga inda ya ke zaune ba.

Rashin dacewar inda Akpabio ke zaune ce ta sa Saraki ya ce ba zai bari ya yi magana ba.

“Sanata ka ke ko tsohon Shugaban Marasa Rinjaye, kai ma ka san bai yiwuwa na bar ka ka yi magana daga inda ka ke, saboda ba wurin zaman ka ba ne. Idan ka na so ka yi magana, to ka koma wurin zaman ka ka zauna.” Inji Saraki.

Daga nan sai Saraki ya umarci Shugaban Masu Rinjaye, Ahmed Lawan da ya ci gaba da karanto batutuwan da ke gaban majalisa.

Sai dai kuma maimakon Lawan ya ci gaba da karanto sauran batutuwan, sai ya shiga cikin rigimar, inda ya goyi bayan Akpabio.

“Shin don ya zabi ya zauna can inda ya ke a yanzu sai me? Ka bar shi ya yi zaman sa mana. Ai can inda ya ke babu makirfo shi ya sa. Bai kamata wani da ciwon kai mu da sha masa kwarorin Panadol ba. Don ana ganin bai fi sauran watanni shida ko bakwai mu kammala zangon mu ba, ai ya kamata a rika yin abin da ke daidai.” Inji Sanata Ahmed Lawan.

Ai nan da nan sai majalisa ta kaure da kuwwa, ba mai jin abin da kowa ke cewa, kowa na kokarin kare dan jam’iyyar sa.

Dukkan kokarin da Shugaban Majalisa Saraki ya yi domin kwantar da hargitsin bai yi nasara ba.

Domin sai da ta kai wasu sanatoci na tashi daga kan kujerun su, su na tsallakawa su na nuna juna da yatsa su da wadanda su ke cacar baki da juna.

Saraki ya zama shugaba a karkashin APC, amma ya koma PDP. Yayin da shi kuma Akpabio daga PDP ya koma APC.

Share.

game da Author