Kungiyar Tarayyar Turai da Bankin Inganta Al’umma na kasar Faransa sun sha alwashin samar da taransifoma mai karfin 330KVA a garin Daura, domin kara karfin wutar lantarki, a garin na Shugaba Muhammadu Buhari.
Kamfanin Raba Harken Lantarki na Najeriya, TCN ne ya bayyana haka ta bakin jami’in su Wale Adeyemi.
Ya bayyyana haka jiya Talata a lokacin da ya ke duba wurin aikin wutar lantarki inda za a kafa taransifoma din.
Ya ce za a kara karfin lantarki a Karamar Hukumar Daura din ne daga 100KVA zuwa 330KVA yadda za a rika samun wuta a ko da yaushe a yankin.
Ya ce gwamnatinn tarayya ce za ta dauki nauyin aikin, tare da taimakon Kungiyar Tarayyar Turai, Bankin Faransa da kuma wasu kungiyoyin bada tallafi. Idan aka kammala aikin, Adeyemi ya ce tattalin arzikin yanki zai bunkasa sosai.
Ya ce za su tabbatar an kammala aikin cikin lokaci, tare da shan alwashin turo ma’aikata da kayan aiki domin fara aikin nan ba da dadewa ba.