Gwamnati ta yi tir da kisan ma’aikaciyar ‘Red Cross’ Hauwa Liman da Boko Haram suka yi

0

Gwamnatin Najeriya ta yi tir da kisan ma’aikaciyar Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC) Hauwa Liman da Boko Haram suka yi a yau Litini.

Ministan yada labarai Lai Mohammed ya sanar da haka a Abuja inda ya jajanta wa iyaye da yan ‘uwan Hauwa Liman.

Ya kuma mika godiyarsa ga gwamnatocin duniya kan saka bakin da suka yi don ganin a ceto wadannan ma’aikata da Boko Haram suka kama.

” Gwamnatin Najeriya ta yi iya kokarin ta wajen ganin Boko Haram sun sako wadannan mutane da suka kama sai dai hakan bai haifar mana da da mai ido ba.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadi ne Boko Haram ta fitar da sanarwar cewa cikin awa 24 za su kara bindige ma’aikaciyar Red Cross daga cikin wadanda suka kama.

Shugaban Kungiyar mai kula da ayyuka a yankin Tafkin Chadi, Mamadou Sow ya ce Boko Haram sun kama Hauwa Mohammed , Alice Loksha da Saifura Khorsa a watan Maris. Inda bayan watanni shida da kama su Boko Haram suka kashe Saifura cikin Satumba.

” Boko haram sun kama ma’aikatan ICRC ne yayin da suke aikin bada agaji a sansanin gudun hijira da ke Rann, sannan sune kuma ke tsare da Leah Sharibu’’.

A dalilin haka Sow ya roki Gwamnatin Tarayya da masu fada aji da su sa baki domin ceto sauran da ke hannu Boko Haram.

Sai dai duk wannan roke roken bai haifar wa kasa da ICRC da da mai ido ba domin Boko Haram sun bindige Hauwa Liman.

Share.

game da Author