Gwamnati ta yaba wa aiyukkan inganta kiwon lafiya da NSHIP ta yi a kasar nan

0

Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko (NPHCDA) na kasa Faisal Shuaib ya bayyana cewa gwamnati ta yaba wa aiyukkan inganta fannin kiwon lafiya da shirin ‘Nigeria State Health Investment Project (NSHIP) ta yi kasar nan.

Shuaib ya fadi haka ne ranar Talata a Abuja inda yace NPHCDA ce ta kafa wannan cibiyar domin tsara hanyoyin shawo kan matsalolin da fannin kiwon lafiyar kasar nan ke fama da su.

Ya ce tun da aka fara shirin a 2013 shirin ta yi aiki a jihohin Ondo, Adamawa da Nasarawa sannan mutane miliyan 16 a kananan hukumomi 35 da cibiyoyin kiwon lafiya 1887 suka amfana da shirin.

Jami’in shirin Joseph Shu yace a dalilin kafa wannan shiri gwamnati ta sami damar shawo kan matsalolin da fannin kiwon lafiya ke fama da su a kasar nan.

Share.

game da Author