Gwamnan Jihar Ogun, Ibekunle Amosun, ya ci gaba da bayyana rashin jin dadin yadda Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshimhole da Bola Tinubu suka hada kai, suka fitar da sakamakon zaben fidda gwani na bogi da kuma magudi, wanda aka bayyana Dapo Abiodun a matsayin dan takarar gwamnan jihar Ogun na APC, a zaben 2019.
Amosun a cikin fushi ya kira Oshimhole da tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Tinubu da sukan mazambata kuma ‘yan kakudubar da suka yi kulla-kullar shirya magudin zabe.
Gwamnan Amosun ya yi wannan kakkausan zargi a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, jim kadan bayan ya gama rantsar da da sabon Babban Mai Shari’a na jihar Mosunmola Dipeolu, a cikin ofishin sa a Abeokula, babban birnin jihar.
Ya ce ko shiru din da su Tinubu da Segun Osoba suka yi a kan batun, ya nuna cewa da hannun su dumu-dumu cikin harkallar tsaida dan takarar gwamna a jihar Ogun.
“Shugaban Kasa na sane da cewa ba a yi zaben fidda gwani na APC a jihar Ogun ba. Sun dai je Lagos ne suka rubuta sakamakon zabe na bogi kawai. Idan har Kwamitin Gudanarwar Jam’iyya na Kasa ya ce an yi zabe, to ba zabe aka yi ba, dodorido kawai aka yi. Wannan abin da na tabbatar kenan.
Amosun ya ci gaba da jaddada cewa karya su Tinubu ke yi, ba a yi zaben fidda gwanin da har za a ce Abiodun ne dan takarar jam’iyyar APC a jihar Ogun ba.