Gidauniyar Aisha Buhari na gina asibitin Mata a garin Yola

0

Gidauniyar uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta kusa kammala ginin asibitin mata da aka fara a cikin asibitin ‘Federal Medical Center’ dake Yola Jihar Adamawa.

Jami’in gidauniyar Kamal Muhammad ne ya bayyana haka inda ya kara cewa sun fara ginin a cikin wannan shekarar sannan sun sa ran kammala ginin kafin shekaran nan ya kare.

Muhammed ya bayyana cewa Malama Buhari ta fara gina wannan asibitin ne domin samar wa matan jihar Adamawa da ingantaciyyar kulan da suke bukata.

Ya ce asibitin zai dauki gadaje 70 da wurin jiran ganin likita da zai dauki mutane 200 sannan mata za su sami kula a fannin awon ciki,bada dabarun tazaran iyali,cututtukan da suka shafi al’auran mata da dai sauran su.

Share.

game da Author