Idan ba a manta ba a watan Satumba ne alkalan gasar rubutun gajerun labarai ta mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, suka bayyana ‘Ya Mace’, a matsayin labarin da ya yi zarra cikin labarai sama da 300 da aka mika don fafatawa a gasar.
Safiyyah Jibril ne ta lashe gasar da labarinta mai suna ‘Ya Mace’.
Safiyya wadda malamar makarantar sakandare ce mai shekara 29 ta cira tuta ne bayan alkalan gasar sun gamsu da bajinta da kwazon ta a rubutun da ta mika.
A cewar alkalan gasar, wannan labarin ya ciri tuta ne saboda ya yi nauyi a galibin ma’aunan da aka yi amfani da su don tantance labarai 25 din da suka duba.
“Labarin ya tabo wata matsala da ke faruwa a wannan zamanin, inda iyaye ke Allah-Allah su aurar da ‘ya’yansu mata.
Safiyyah Jibril malamar makarantar sakandare ce, kuma daliba mai karatun digiri na biyu, wato Master’s, a fannin Kimiyyar Kasar Noma a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.
Marubuciyar labarin Sunanmu Daya, Sakina Lawal ne ta zo na biyu a gasar. Tana da takardar digiri a fannin Harshen Hausa daga Jami’ar Jihar Kaduna.
Sanna sai wacce ta zo ta uku a gasar, Bilkisu Muhammad da labarin ta mai taken” Zaina”. Yanzu haka daliba ce a Jami’ar Bayero ta Kano, inda take karatun Shari’a, wato Law.
Shugaban BBC Hausa, Jimeh Saleh, ya bayyana cewa BBC ta shirya wannan gasa ne don ta karrama mata da basu daman fafatawa a gasar rubuce-rubuce.
An yi wannan buki ne a dakin taro da ke Otel din Sheraton dake Abuja sannan ya samu halarta baki da dama.
