Daidai karfe 10:15 na dare aka bai wa kowane dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP dama ta minti uku kacal ya fito ya tsaya kan dandamali dominn ya yi wa dubban masu zabe takaitaccen jawabi.
An yi wa kowa uzirin cewa amma kada ya wuce minti biyar, domin jama’a sun zaunu sosai a wurin.
An fara kiran sunayen ‘yan takara daya bayan daya su na fitowa su na yin jawabi, su na komawa su zauna.
*An rika yin kiran ne a haruffance, wato wanda sunan mahaifin sa ya fara da ‘A’ shi aka fara kira, aka kammala da wanda sunan ta ya fara da ‘T’.
Hakan ya sa aka fara kiran Tsohon Mattaimakin Shugaban Kasa, Atiku, wanda sunan mahaifin sa ya fara da ‘A’. Sannan kuma an kammala da Tanimu Turaki, wanda sunan mahaifin sa ya fara da ‘T’.
Na biyu da aka kira, Datti Baba-Ahmed bai samu karasawa ya yi jawabin sa ba, domin an kira sunan sa aka ji shiru. Nan da nan kuma aka yi sanarwa cewa ya na waje cinkoson jama’a ya kawo masa cikas din shiga filin taron da wuri. An bada uzirin cewa idan ya shigo za a ba shi dama ya yi nasa takaitaccen jawabin.
ATIKU ABUBAKAR:
“Wannan rana ce mai dimbin tarihi, wadda makomar wannan kasa na hannun ku wakilai masu jefa kuri’a. Domin ku ne za ku zabi wanda ku ke so ya zama shugaban kasa. Ya zama dole ku zabi wanda ya cancanta. Shekaru hudu da suka gabata an yi canji a kasar nan, amma jama’a ba su ji dadin canjin da aka yi ba. Wannan canji bai haifar da komai ba sai matsin halin rayuwa, yunwa, rashin aiki da kuma kara raba kawunan ‘yan Najeriya.”
Daga nan ya yi bayanin cancantar sa da kuma yadda zai tsamo Najeriya daga cikin mawuyacin halin da ya ce ta afka a ciki.
ATTAHIRU BAFARAWA:
Na karade kasar nan ina kamfen na neman kuri’un ku wakilai masu zabe. Ba jirgi na rika hawa ina lulawa sama ba. A mota na rika karade jihohin kasar nan, kuma na ga irin yadda titina suka lalace a fadin Najeriya. Idan aka ba ni dama, zan maida hankali sosai wajen gyaran titina. Zan zama shugaba na Najeriya ba na wata kabila ko bangare ko wasu mabiya addini daya ba. Ba zan yi fushi da sakamakon zaben da za a yi yau ba. Duk wanda Allah ya ba, zan goya masa baya, zan bi shi.”
RABI’U KWANKWASO:
“Bari na fara da bai wa PDP hakauri, domin a baya mun ce ta shiririce,har muka fice. Yanzu kuma ta gyaru, domin dukkan mu da muka fusata muka je aka kafa gwamnatin APC da mu, mun dawo. Ya kamata PDP ta ba Buhari lambar kyautar gyara PDP da ya yi, har ta zama bazawarar da kowa ke neman ya aura a yau.
“Ina kira ga wakilai masu zabe su zabi wanda suka san idan ya ci takara kuma zai iya cin zabe, ba wanda kawai zai iya cin takara ba.”
Kwankwaso ya yi bayanin abubuwan da zai yi har da jan ‘yan jam’iyya da kowa a jika, kawar da kabilanci da kara hadin kan kasar nan. Ya tunatar da yadda a zaben 2011 na fidda gwanin APC, ya zo na biyu, bayan Muhammadu Buhari.
SULE LAMIDO:
“A wannan rana mai matukar muhimmanci akwai babban aiki ga wakilai masu zabe, shi ne zaben wanda ya fi cancanta, kuma zabe ne na aiki da hankali ba aiki da son rai ba. Cikin shekaru 19 PDP ta shahara kuma ta samu tawaya daga baya. A yanzu kuma ta sake farfadowa, har kowane bazawari na neman auren ta a yau. Idan ku ka yi zabe na son rai, to za ku warware tufkar PDP, amma idan ku ka yi aiki da hankali da tunanin ku a wurin zabe, to hakan ne mafi dacewa a gare mu baki daya.
“Ina kira da ku zabi cancanta. Ina sanar da ku cewa ku ne madubi na, ni ne madubin ku. Ni ne dan takarar da ya cancanta ku jefa wa kuri’a.”
AHMED MAKARFI
“Alamomi na nuna cewa jam’iyyar PDP ce gwamnati mai jiran gado a zaben 2019. A baya ana cewa jam’iyyar mu ta mutu, amma yanzu yanzu ta farfado kuma ta wartsake da karfin ta. Na fito takara ba don na taka rawa wajen farfado da PDP ba a lokacin da na ke shugabancin riko. Ko da na fadi zabe b azan yi bakin ciki ba, zan yi murna don a yau jam’iyyar mu ta farfado har ta kama hanyar sake kafa gwamnati.
“Batun sake fasali dama can akwai shi cikin tsarin jam’iyyar PDP. Don haka za mu sake tsarin jam’iyyar mu kuma idan aka ba ni dama za mu yi shugabanci nagari, ba irin shugabancin da ya haifar da kiyayyar juna a cikin ‘yan Najeriya, wanda APC ta ruruta ba.”
DAVID MARK
“A karkashin wannan mulki kasar nan an haifar da rabuwar kawunan jama’a. Zan y i kokari cikin kankanen lokaci na sake hada kan ‘yan Najeriya. Ina da tsare-tsare da manufofi da kudirori wadanda idan na hau kuma na yi amfani da su, to a cikin kwanaki 730 zan sake farfado da tattalin arzikin Najeriya.
“PDP jam’iyyar mu ce, ko da na fadi ba zan fita ba kuma ba zan fusata ba. Zan goyi bayan duk wanda ya yi nasara domin sake kafa gwamnatin da za ta share wa jama’a hawaye.”
BUKOLA SARAKI
“Mun samu kan mu cikin wani mawuyacin halin haruwar kawuna da ruruta kabilanci da rikice-rikice a lokacin gwamnatin APC. Fatara da yunwa sun zama tsumagiyar kan hanya, dukan kowa suke yi. Tattalin arziki ya karye. Ina kira ga wakilai masu zabe sub a ni dama domin na yi amfani da kwarewa ta, na dawo da kasar nan turba hadin kan al’ummar Najeriya da kuma inganta tattalin arziki da tsaro.”
AMINU TAMBUWAL
“Najeriya na bukatar shugaba, jagora, wanda zai hada kan kasar nan, wanda al’umma suka amince da shi, domin a yanzu an ruruta wutar gaba da kiyayya da rabuwar kawuna a zukatan ‘yan Najeriya. Ina da gogewa da kwarewar sanin makamar mulki, kuma nin kwararren lauya ne. ko ban yi nasara ba, zan goyi bayan wanda Allah ya ba nasara domin mu taru mu hada kai, mu ceto Najeriya.”
TANIMU TURAKI
“Bambancin kabila, rikice-rikice da bangaranci sun yi katutu tun daga shigowar wannan gwamnatin ta APC. Idan ana neman wanda ya cancanta, to ga ni. Idan ana neman mai kishi, to ga ni. Idan ana neman mai gaskiya, to ga ni. Idan ana neman mai rikon amana, to ga ni. Domin idan aka zabe ni sai na yi aiki nunki dubu bisa ga wanda gwamnatin APC ta yi a cikin shekaru hudu.”
Discussion about this post