Fayose ya maka EFCC kotu

0

Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya maka Hukumar EFCC kotu, saboda ta dora sunan sa a cikin wadanda jami’an tsaro ke sa-idon ganin sun cafke su idan sun nemi ficewa daga kasar nan.

Gwamnan wanda zai sauka daga mulki cikin mako mai zuwa, ya na neman kotu ta bambarar masa naira biliyan 10 daga hannun hukumar ta EFCC, saboda bata masa suna da ta yi.

Ya ce abin da EFCC ta yi masa ya karya kuma ya tauye masa ‘yanci, saboda a lokacin da EFCC ta bayyana sa-ido a kan sa, ya na da rigar kariya ta mulki, wadda kowane gwamna ke sanye da ita.

Fayose ya ce dora sunan sa a jerin sunayen wadanda ake farauta, tare da iznin kamawa idan sun nemi ficewa daga kasar nan, ya tauye masa hakki, kuma ya janyo masa tozartawa da zubar da kima da mutunci a idon jama’a. Ya kuma kara da cewa hakan da EFCC ta yi masa, wata bahaguwar doka ce aka shigo da ita kasar nan da rana tsaka.

Lauyan Fayose Obafemi Adewale, ya rubuta wa EFCC wasika a ranar 3 Ga Satumba, 2018 cewa ya ba hukumar sa’o’i 72 ta janye umarnin da ta ba jami’an tsaro cewa su kama Fayose idan sun same shi zai fita kasar nan a filin jirgin sama, tashar jiragen ruwa, ko kuma a kan iyakar kasar nan a mota.

Lauyan ya kuma nemi EFCC ta ba Fayose hakuri, wanda ya ce a wasu manyan jaridun kasar nan za a buga ban-hakurin da kuma soshiyal midiya.

Kakakin yada labaran Fayose, Lere Olanikan, ya ce an yanke shawarar maka EFCC kotu ne, ganin cewa wa’adin da aka ba hukumar na ta janye umarnin kama Fayose din ya wuce, amma ba ta yi komai ba.

Ranar 16 Ga Yuli ne EFCC ta fitar da sanarwar cewa ta na rokon idan Fayose ya nemi ficewa kasar nan, to a damke shi.

Share.

game da Author