Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti da ya sauka daga mulki jiya litinin, Ayo Fayose ya kai kan sa ofishin Hukumar EFCC kamar yadda ya yi alkawari zai yi idan ya sauka daga mulki.
Fayose ya cika alkawarin sa, inda ya bayyana EFCC cikin awa 24 bayan saukar sa daga mulkin jihar Ekiti.
Sai dai kuma Fayose ya kwashi tawagar ‘yan kallo yayin da ya isa ofishin EFCC a yau Talata tare da dandazon wasu gaggan jam’iyyar PDP, ciki har da Gwamnan Jihar Ekiti, Nyesom Wike da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode.
Fayose ya shiga EFCC ya na sanye da singileti mai dauke da kalmar Turanci mai bada ma’anar: “To EFCC, ga ni na zo.”
Fayose ya na dauke da jikuna biyu masu nuna alamar cewa su na dauke da kayan da zai bukata a zaman da zai yi a ofishin EFCC, da suka hada har da tabarmar kwanciyar da kamar yadda ya ce zai tafi da su.
Dama tun kwana hudu baya Fayose ya ce jami’an tsaro sun kulle masa asusun ajiyar na banki da sauran nau’o’in kuntata masa.
Har zuwa lokacin da ake rubuta wannan labari da Fayose na ofishin EFCC ya na shan tambayoyi.
FAYEMI YA ZAMA GWAMNA KARO NA BIYU
A yau ne kuma yayin da Fayose ya kai kan sa ofishin EFCC, ana can ana bikin rantsar da sabon gwamna Kayode Fayemi a karo na biyu. Fayemi dai ya sha kaye ne shekaru hudu da suka gabata daga hannun Fayose, wanda shi ma a lokacin sake komawa ya yi a zango na biyu bayan ya yi gwamnan da farko.
Sai dai ba kamar Fayose ba, yayin da aka kayar da Fayemi shekaru hudu da suka gabata, Fayose ya kafa masa kwamitin bincike, kuma aka buga masa Farar Takardar da aka same shi da laifin wawurar kudade.
Fayemi ya yi tsalle-tsalle daga wannan kotu zuwa waccan domin kada a tuhume shi.
Har yau maganar ta na kwan-gaba-kwan-baya.
Ba a gurfanar da Fayemi ba, sai ma ya shiga jam’iyyar APC, a karkashin mulkin Muhammadu Buhari, ya sake tsayawa takara, kuma ya yi nasara, a zaben da aka shaida cewa an tafka magudi.
Discussion about this post