EL-RUFAI: Yabon Gwani ya zama dole, Daga Aisha Yusufu

0

Mutane da dama musamman mazauna jihar Kaduna sun fada cikin rudani a dan makonni biyu da suka gabata. Tun daga barkewar rikici a garin Kasuwan Magani da yayi sanadiyyar rasuwar mutane da dama zuwa garkuwa da aka yi da sarkin Adara Maiwada Galadima da yayi sanadiyyar mutuwar sa, sannan kuma da rashin zaman lafiya da aka yi fama dashi a fadin jihar ya sa mutane da dama sun fada cikin dimuwa da fargaba a wadannan lokutta.

Sai dai kuma abin da ya burge mutane da dama a fadin jihar da kuma canja ra’ayoyin mutane da dama bisa ga tunani da irin matsayin da suka sa gwamnan jihar wato Nasir El-Rufai ya sauya matuka bisa ga kwazon aiki da ya nuna wajen dakile rikicin.

A karon farko jihar ta samu gwamnan da ya kasa tsugune don ganin rikici a jihar bai fi karfin gwamnanti ba kamar yadda yakan faru a da, da sai an yi kashe-kashe sannan an kona muhallai da dakunan bauta kafin a kawo wa mutane dauki, wannan karon gwamna El-Rufai ya yi namijin kokari wajen ganin hakan bai faru ba.

Da kansa ya rika fita titunan jihar, kwararo-kwararo yana tabbatar da ana bin doka sannan kuma mutane basu dauki hukunci a hannun su ba.

Mazauna da unguwannin Kaduna dama suna shiga cikin rudani da tashin hankali ganin cewa dama jihar kamar kwai ce jira kawai take yi a taba ta ta fashe sai gashi abin bai zamo haka ba.

Gwamna ya fadi a kafafen yada labarai a jihar cewa wannan karon gwamnati ba zata nade hannunta ta zuba wa mutane ido ba. Duk wanda aka kama da laifi zai dandana kudar sa. Sannan ya kara da cewa unguwanni kamar su Gonin Gora da suke tare matafiya basu ji ba basu gani ba su kashe wasu ko su illata su zai yi maganin su.

Haka kuma ya ce duk wani unguwa da suka ki hada kai domin a samu zaman lafiya gwamnati za ta yi maganin su.

A haka ne mutane da dama suka yaba wa gwamnan bisa kokarin da ya yi wajen ganin rikicin bai karade gari ba.

Gwamna El-Rufai ya sha luguden ruwan goma ta arziki ba daga mutanen jihar Kaduna ba har da wadanda suke makwabtaka da jihar bisa namijin kokari da yayi a jihar da kuma jan kunnen da yayi wa mutanen jihar saboda gaba.

Share.

game da Author