Hukumar Hana Cin Hanci da Zambar Kudade (EFCC) ta nada sabon shugaban ta da zai kula da shiyyar Gombe.
An nada Friday Ebelo, wani kwararren mai bincike da ke da mukamin sufurtanda.
Kakakin Hukumar da ke Gombe, mai suna Bello Adamu ne ya bayyana haka ga manema Labarai jiya Talata a Gombe.
Adamu ya ce Ebelo ya karbi ragamar jagorancin ne daga Johnson Babalola, wani mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, wanda aka yi wa canjin wurin aiki zuwa hedikwatar ‘yan sanda a Abuja.
Ya kara da cewa Ebelo na daya daga cikin ma’aikatan hukumar EFCC da aka fada dauka tun bayan kafa hukumar shekaru 14 da suka gabata.
Kafin a nada Ebelo shugabancin shiyyar Gombe, shi ne shugaban bangaren binciken harkallar 419 a hedikwatar EFCC a Abuja.