EFCC ta musanta zargin barin wadanda ta ke tsare cikin yunwa

0

Hukumar EFCC ta musanta zargin da aka yi cewa ta na barin wadanda ta ke tsare da su cikin fama yunwa ba tare da an rika ba su abinci a kai a kai ba.

Kakakin Yada Labaran Hukumar, Wilson Uwujaren ya fadi haka, inda ya jaddada cewa hukumar na barin iyalan duk wanda ke tsare din su na rika kai masa abinci a kowace rana.

Ya bayyana haka ne ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, jiya Talata a Lagos.

Uwujaren ya yi wannan raddi ne ga Kungiyar Kare Hakkin Musulmai ta Najeriya, MURIC wadda ta yi wannan zargin.

Shugaban Kungiyar ne Ishaq Akintola ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya ciyar da wasu da ke tsare a EFCC, har su 150, a zaman da ya yi a tsare a can na wasu ‘yan kwanaki.

Uwujaren ya bayyana wa NAN cewa ba shi da masaniyar ko Fayose ya ciyar da mutane 150 da ke tsare a EFCC.

Share.

game da Author