Dalilin da ya sa na bi tawagar shirya Obasanjo da Atiku – Sheikh Gumi

0

Babban shehin malamin addinin musuluncin nan mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa babu siyasa a raka Atiku wurin Obasanjo da yayi.

Gumi ya ce a matsayin sa na babban malami wasu da ga cikin abinda ya dace yayi shine ya shirya mutanen da basu da jituwa a tsakanin su.

” Shirya mutane biyu da basu da jituwa a tsakanin su aikin ibada ne kuma a matsayina na malamin addini tilas mu rika yi muna shirya mutanen da basu ga maciji a tsakanin su. Idan ba mu yi haka ba ba mu yi wa addini adalci ba.

” An neme ni da in shiga cikin wannan tawagar da za su tafi wajen sasanta Atiku da Obasanjo ne a matsayi na malami mai fadar gaskiya. Ni dama kowa ya sani babu wata jam’iyya da na ke bi. Duk jam’iyyar da ta kafa gwamnati sannan ta yi abinda bai da ce ba zan fito in fada mata gaskiya.

” Idan ba a manta ba a lokacin mulkin PDP na ragargaje ta bisa abubuwan da tayi ba daidai ba haka kuma gwamnati mai ci. Ni dai kawai kira ta ga gwamnati shine a yi wa mutane adalci a kowani lokaci

Gumi ya kara da cewa dole ne irin su malaman addini su shiga gaba wajen shirya wadanda basu da jituwa a tsakanin su musamman shugabanni.

Share.

game da Author