Daliban Chibok shida kadai ne aka gani a Sambisa – Inji iyayen su

0

Iyayen daliban Chibok mata ‘yan sakandaren da aka sace tun cikin 2014, sun bayyana cewa shida ne kadai aka gani a Dajin Sambisa kwanan nan, ba 57 da wasu kafafen yada labarai suka rika bugawa ba.

Kakakin Yada Labaran Iyayen Yaran mai suna Ayuba Alamson ne ya bayyana haka ga manema labarai a Maiduguri, cewa wata mataa da ke tsare, amma ta kubuta daga hannun Boko Haram, ta tabbatar da cewa ta na wuri daya ne da wasu ‘yan matan shida wadanda ake tsare da su a wuri daya.

Alamson wanda ya bayyana sunan matar wadda ta kubuta da Jummai Abouku, ya ce ta tsere ne daga hannun Boko Haram, kuma kwanan nan sojoji suka damka ta ga hannun iyayen ta bayan an tabbatar da tantance ta.

Ya kara da cewa an sace Jummai tare da babban dan ta daga cikin ‘ya’ya shida da ta ke da su a Askira Uba cikin 2014.

Jummai ta shaida wa manema labarai cewa an tsare ta tare da wasu matan Chibok shida, kuma duk ta gane su, kuma ta gane iyayen su.

Ta ci gaba da shaida wa manema labarai cewa duk an aurad sa ‘yan matan ga ‘yan Boko Haram, kuma akwai wadda ta baro dauke da tsohon ciki, wata kuma ta haihu, sauran hudun kuma tun da aka aurad da su din har yau ba su yi ciki ba.

Alamson ya bayyana cewa ita ma Jummai din an aurad da ita ga wani dan Boko Haram watanni kadan kafin ta tsere.

Ta kubuta ne tare da babban dan ta da aka tsare su tare, inda sojoji suka ajiye su a sansanin gudun hijira na Bama. Amma daga baya-bayan nan an damka ta a hannun iyayen ta, ita da dan ta a Chibok.

A karshe Alamson ya ce har yanzu ba su fitar da rabon dawowar sauran matan da ba, idan da rabo da kuma yawan rai.

Share.

game da Author