A yau ne ake sa ran jam’iyyar APC da sauran jam’iyyun da ba su bada sunayen ‘yan takarar su na zabukan 2019 ba, za su bayar ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
INEC ta bada sanarwa yau ne 18 Ga Oktoba, ranar rufe karbar sunayen ‘yan takara, kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta 2010 ta gindaya.
A yau za a rufe karbar sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da na majalisar dattawa da na tarayya. Ranar 2 Ga Nuwamba kuma a rufe karbar na gwamnoni da na majalisar jihohi.
INEC ta ce har zuwa Talata da ta gabata, jam’iyyu takwas ne kacal suka damka mata sunayen ‘yan takarar su, daga cikin jam’iyyu 91cda suka yi rajista.
Jam’iyyar APC wadda ita ce jam’iyya mai mulki, ta fi kowace jam’iyya shiga cikin rigingimun tsaida ‘yan takara.
A yanzu da ya rage saura yini daya cur a rufe karbar sunayen ‘yan takara, jam’iyyar APC da magoya bayan ta na jihohin Adamawa, Zamfara, Delta da Kaduna da sauran jihohi da dama ba su san ‘yan takarar da za su wakilce su ba.
ADAMAWA
A jihar Adamawa ‘yan takara biyu da suka kalubalanci Gwamna Jibrilla Bindow a neman tikitin takarar gwamna, wato Nuhu Ribadu da Mahmud Ahmed, sirikin Shugaba Muhammadu Buhari, sun zargi uwar jam’iyya da goyon bayan gwamna Bindow aka bayyana shi a matsayin dan takara.
Har zuwa yanzu da dama a cikin jam’iyyar a Jihar Adamawa ba su san takamaimen idan Bindow din ne aka tsaida ba.
A Abuja kuma da dama daga cikin jiga-jigan gwamnati na tababar biyayyar Bindow ga APC, ganin yadda ubangidan sa kuma dan asalin jihar sa, Atiku Abubakar ya fito takarar shugaban cin kasar nan.
Duk da Bindow ya fito ya ce biyayyar sa ga Buhari ta ke ba ga Atiku ba, ana tsoron kada Bindow ya yi wa Buhari ‘anti-party’ a zaben shugaban kasa.
JUMMAI ALHASSAN
Haka ta faru ga tsohuwar Minista Jummai Alhassan, wadda duk da ta dawo ta ce Buhari ta ke yi ba Atiku ba, an hana tantance ta a zaben fidda gwani na takarar gwamna a jihar Adamawa,mita kuma ta fice daga jam’iyyar, har a jiya Laraba ta je ofishin APC na jihar Adamawa ta kwashe kayan da ke cikin ofis din karkaf, ta ce dama duk da kudin ta ta gyara ofis din, ba da kudin jam’iyyar APC ba.
BINTA GARBA
An bayyana Binta Garba ce ‘yar takarar sanata ta Adamawa ta Arewa, amma daya daga cikin ‘yan takara, mai suna Ahmed Idris, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa karya ake yi ba a gudanar da zaben fidda gwanin ba, ballantana har a ce Binta ce ta yi nasara.
“Mun dade cikin jam’iyya mu na kashe kudaden mu wajen yakin neman zabe. Binta kuma ko sisi ba ta kashe ba. Sai ana gobe zabe aka ce mana ita za a tsaida takara. Ta yaya za mu yarda? Wannan adalci ne?”
“Ko a wancan zamani na PDP ba a yi irin wannan kakudubar ba. Adalci aka ce Buhari zai shimfida idan ya hau. Shi ya sa aka zabe shi. Ba don haka ba kuwa da Jonathn bai yarda shi ma an kayar da shi ba idan haka ne.” Inji Idris.
Idris ya ce ya kashe sama da naira miliyan 150 a wajen kamfen, kuma akwai irin su da aka yi wa wannan rashin adalcin sama da su 1000 a kasar nan.
“Ni ban san ta yadda APC ke so ta ci zabe a 2019 ba. Ma ji ma gani idan zaben 2019 din ya zo!”
Baya ga matsalar zaben dan takarar sanatan Adamawa ta Arewa, akwai rigingimun zaben fidda gwani na majalisar tarayya sosai daga jihar.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=mPq9c1rqSYo&w=560&h=315]
KADUNA
A jihar Kaduna har yau ana neman yin katankatana ko batan-bakatantan dangane da sahihancin dan takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya, tsakanin Sanata Shehu Sani da kuma dan gaban goshin Gwamna Nasir El-Rufai, Uba Sani.
Yayin da APC a Abuja ta ce Shehu Sani ne dan takarar ta, a gefe daya kuma Uba Sani na ikirarin shi ne dan takara ba Shehu Sani ba.
ZAMFARA
A wannan jiha ce APC ta fi fama da rikicin da ke neman zame mata karfen kafa, domin tuni ma INEC ta bayyana wa APC cewa kada ma ta bata lokacin kai mata sunayen ‘yan takara, tunda ba a yi zaben fidda gwani a jihar ba.
INEC ta yi wancakli da zaben fidda gwanin da gwamnan jihar Zamfara ya shirya da kan sa, kuma duk shi da ‘yan bangaren sa ne ya ce sun yi nasara.
Sai dai kuma shugaban jam’iyyar APC Adams Oshimhole ya ce su babu ruwansu, za su mika wa INEC sunayen dukkan ‘yan takarar APC na jihar Zamfara.
Yayin da APC ta ce an yi zabe, INEC ta ce karya ce ba a yi ba.
Daga baya APC ta ce a n cimma yarjejeniya, har ila yau daya daga cikin ‘yan takarar, Sanata Kabiru Marafa y ace ba a yi wani sulhu ba, idan ma an yi to bai san an yi din ba.
Shekaranjiya ranar Litinin ne kuma INEC a ta bakin shugaban ta Mahmood Yakubu ta kara jaddada matsayin ta cewa APC ba za ta shiga zabuka ba daga jihar jihar Zamfara.
Sai dai kuma wani rahoto daga Babbar Kotun Jihar Zamfara ya hana INEC da APC soke wani dan takara daga jihar Zamfara.
Mai Shari’a Mukhtar Yusha’u ne ya bada wannan umarnin a ranar Talata, bayan da shugabannin jam’iyyar na APC na jihar Zamfara suka shigar da kara a gaban sa.
Za a jira a gani shin INEC za ta bada kai bori yah au, ko kuwa ya za a karke?
NEJA
Daga cikin ‘yan takarar Majalisar Tarayya daga jihar Neja, daya ne tal aka bada sanarwar cewa ya ci zabe daga jihar, duk sauran ana nan ana ta gumuzu da tataburza.
Amma kuma an bayyana sakamakon zabukan sanatocin jihar uku.
Akwai rashin jiyuwa sosai tsakanin gwamna Abubakar Bello da ‘yan majalisar tarayya. Hakan kuwa ya biyo haushin gwamnan da suke ji sakamakon kayar da sanatoci biyu da ka yi a zaben fidda gwani, wato sanata David Umaru da Sabi Abdullahi.
Kwanishinan Kananan Hukumonin Jihar Neja ne Zakari Jikantoro aka ce ya kayar da David Umaru.
DELTA
A jihar Delta kuwa akwai matsala a kwance, domin kotu ta datakar da jam’iyyar APC daga mika sunayen ‘yan takarar ta a zaben 2019, ga Hukumar Zabe a Abuja.
Babbar Kotun Tarayya ta Asaba ce da kan ta ta bayar da wannan umarni biyo bayan karar da aka shigar.
Mai Shari’a Toyin Adegoke ce ta hana a mika sunayen, saboda Kwamitin Zartaswa na APC ya maka uwar jam’iyya da Adams Oshimhole da INEC kara a kotu.
Babbar barazana a nan ita ce a jiya mai shari’a ya bayar da wannan umarni, ana gobe za a mika sunayen ga INEC.