Da harkalla Buhari ya zama dan takarar APC -Ofishin Kamfen na Atiku

0

Ofishin Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar da zai fafata a karkashin jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa da harkalla aka tsayar da Shugaba Muhammadu Buhari takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.

Sanarwar da ofishin ya fitar jiya Lahadi, ta nuna mamakin yadda Buhari ne kadai dan takarar da aka tantance, duk kuwa da cewa akwai wasu ‘yan karar biyar da ke kalubalantar sa.

Ofishin Yakin Neman Zaben Atiku ya bada wannan sanarwa ce a matsayin martani ga Daraktan Yada Labarai na kamfen din Buhari.

Festus Keyamo ya yi wa zaben da aka yi wa Atiku Abubakar gwalo da gwasalewa cewa an yi amfani da kudi, don haka babu mutunci kamar irin wanda aka yi wa Buhari.

A nasu maida martanin, ofishin na Atiku ya tunatar da cewa an tantance Buhari shi kadai, an ki tantance sauran, wanda wannan tsantsar rashin adalci ne.

Ya ci gaba da cewa zaben Atiku kuwa kowa ya shaida an yi a zahiri, kuma dukkan wadanda aka kayar sun amince, kuma sun taya shi murna.

“Zaben fidda gwanin da jam’iyyar APC ta yi kuwa cike yake da harkalla da rashin adalci, ta yadda har uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta fito ta ce an tafka rashin adalci, an ki tantance ‘yan takara, bayan an yaudare su an sa sun kashe kudi sun sayi fam.”

Daga nan sai ofishin Atiku ya ce abin da har ya kai matar Buhari ta tabbatar da rashin adalcin da jam’iyyar Buhari ya tafka, to wa ya fi ta sanin mijin ta?

Share.

game da Author