Cutar ‘Dyslexia’: Kira ga Iyaye da su maida hankali ga ‘ya’yan su

0

Cutar ‘Dyslexia’ cuta ce dake rage karfin kwakwalwar mutum ta inda koyan karatu kan yi wa mai dauke da ita wuyan gaske.

Likitoci sun bayyana cewa cutar kan kama yaro tun yana cikin mahaifiyarsa ne a dalilin rashin samun isasshen sinadarin da ya kamata ya don gina kwakwalwarsa da kyau da kuma matsalolin canjin yana yi da kan shafi mata masu ciki.

Likitocin sun ce alamomin wannan cutar su hada da rashin iya ganin abu da kyau, rashin iya rubuto da gane kalmomi sannan a wasu lokuta har da rashin iya fadan kalmomi yadda ya kamata.

” Rashin sani game da wannan cuta kan sa malamai,iyaye da abokai su guji irin wadannan yara duk da cewa bincike ya nuna suna cewa da yawan su na da kwazo matuka.

A dalilin haka ne gidauniyar ‘Dyslexia’ dake a nan Najeriya ta shirya taro domin wayar da kan mutane musamman malaman makarantu da iyaye game da wannan cuta.

Ben Arikpo shugaban wannan gidauniyar ya ce bincike ya nuna cewa mutane miliyan 32 a Najeriya na dauke da wannan cuta, Sannan daya cikin yara uku da ake haifa kan zo duniya dauke da wannan cuta.

Share.

game da Author