Buhari ya sa dokar fara karbar haraji daga kadarorin ’yan Najeriya a kasashen waje

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannun kan wata Dokar Musamman domin dakile karkatar da kudade zuwa kasashen waje, wadda aka sa wa suna ‘VOARS’.

Wannan sabuwar doka ta musamman ta fara aiki ne tun daga ranar 8 Ga Oktoba, ranar da Shugaba Buhari ya sa mata hannu.

Kakalin Buhari, Garba Shehu, ya bayyana cewa sabuwar dokar ta umarci duk wani dan Najeriya mai wata kadara ko harkokin kudaden shiga a kasashen ketare, to daga nan zuwa watanni 12, zai bayyana adadin abin da ya mallaka, ba tare da an tirsasa shi, sannan zai rika biya wa kadarar ko kudaden shigar haraji a nan Najeriya.

Ya kara da cewa duk wanda ya fito don radin kan sa ya bayyana adadin kadarorin sa ko kudaden shigar sa a kasashen ketare, to zai biya haraji na kashi 1 bisa 3 na abin da ya mallaka ko ribar, a lokaci guda.

Ya kara da cewa idan kuwa har ya bari bincike ya bi ta kan sa, aka gano abin da mallaka din, to zai biya dukkan harajin da bai biya baya ba, wanda zai kasance wasu makudan kudade ne da sai ya ciji lebe.

Shehu ya ce za a bude ofishin VOARS a kasar Switzerland, karkashin sa-idon ofishin Ministan Shari’a, Abubakar Malami.

Share.

game da Author