Akalla sojojin Najeriya 18 ne aka kashe a wani sabon hari da Boko Haram suka kai wa wani sansanin sojoji.
Majiyar soja ba daya ba ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa rugugin wutar da aka bude a sansanin da aka kai harin ta yi muni fiye da yadda jami’an sojoji suka bayyana abin da ya faru.
An kai wannan hari ne tun a ranar Litinin.
An ruwaito daga majiyar cewa akalla an kashe sojoji 18, wasu takwas kuma na asibiti a halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai.
Majiyar kuma ta ce akalla an nemi sojoji 157 amma an rasa inda suke bayan da Boko Haram suka kai hari a Bataliya ta 157 da ke kauyen Metele, cikinn jihar Barno.
Majiyar mu ta ce sojojin da aka nema aka rasa sun hada da masu kananan mukamai da karabiti har su 151, sai kuma ofisoshi su shida.
An kwaso gawarwakin sojojin da aka kashe su 18 da kuma wadanda suka ji ciwo an kai su asibitinn kula da sojoji da ke kilomita 115 daga inda aka kai musu hari.
Majiya ta kara tabbatar mana da cewa ko dai an banka wuta ko kuma an lalata motocin yaki tanka guda giyu da sauran dimbin makamai na sojojin Najeriya.
Dama kuma tun a ranar Litinin din rundunar sojan Najeriya ta yi sanarwa a shafin ta tweeter cewa ana can ana bata-kashi tsakanin sojojin Najeriya da Boko Haram.
Hukumar sojoji a ranar Laraba, ta ce an kashe Boko Haram 76 sojoji bakwai kuma sojoji 16 sun ji rauni.
Amma sojoji ba su ce ga adadin yawan wadanda suka nema suka rasa ba.
Sai dai kuma su kwamandojin sun ce sojoji 18 ne aka kashe, ba 7 ba da hukumar tsaro ta sojojin ta ce an kashe.
Kafin a kai harin dai akwai manyan jami’an soja 15 da sojoji 470 a cikin bataliyar da ke kauyen Metele, amma an yi musu barna bayan da aka yi bincike bayan kai harin.
Discussion about this post